Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 6 A Wani Kauye...

Ta’addanci: ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 6 A Wani Kauye Kusa Da Maiduguri

417
0

‘Yan ta’addan Boko Haram sun hallaka mutane 6 a wani kauye da ke kusa da garin Maiduguri ta jihar Borno.

Mayakan na Boko Haram e sun kai harin a kauyukan Bulama Isa da Dala Wulari da Abbajiri da ke kusa da sansanin ‘yan gudun hijira a Bakassi.

Mazauna garin sun ce ‘yan bindiga sun yi yunkurin shiga sarsanin na Bakassi, amma ba su samu nasara ba, wanda hakan ya sa suka shiga kauyukan yakin tare da kashe wasu mutane shida.

Sai dai kawo yanzu, rundunar sojin Nijeriya ba ta ce uffan a kan faruwar wannan lamari ba.

A ‘yan kwanakin nan dai, mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a kan al’ummomin da ke kusa da garin Maiduguri da kuma sansanin soji da ke yankin.