Home Labaru Bayan Rantsuwa: Akwai Yuwuwar Wasu Ministoci Su Ci-Gaba Da Aikin Su –...

Bayan Rantsuwa: Akwai Yuwuwar Wasu Ministoci Su Ci-Gaba Da Aikin Su – Buhari

290
0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai yiwuwar wasu daga cikin ministocin sa su ci-gaba da aiki a zangon mulkin sa na biyu.

Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na NTA, inda ya kara da cewa ya umurci ministocin sa su kawo masa rahoton ayyukan da su ka yi tsawon shekaru hudu, amma wasu daga cikin su na iya ci-gaba da aikin su.

Shugaba kasa Buhari ya ce, zangon mulkin sa na biyu zai mada hankali ne a bangaren tsaro, musamman abinda ya shafi harkokin ‘yan sanda da kuma ma’aikatar shari’a domin ganin su na aikin su yadda ya kamata.