Home Labaru Kashe-Kashen Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutune 23 A Kauran-Namoda

Kashe-Kashen Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutune 23 A Kauran-Namoda

338
0

Wasu ‘yan bindiga sun sake kashe sama da mutane 20 a wasu kauyuka da ke jihar Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun kai harin ne a wasu kauyuka da su ka hada da Tunga da Kabaje da ke cikin garin Sakiji a karamar hukumar Kauran-Namoda.

Shugaban karamar hukumar Kauran Namoda Lawal Isa Abdullahi ya ce ‘yan bindigan na haye ne a kan Babura, inda daga isowar su sai suka fara harbin mai kan uwa da wabi.

Wani mazaunin kauyen mai suna Aliyu Yushau, ya ce wasu jami’an ‘sa-kai ne su ka tare wani babur da aka goyo Iyalin wani ‘dan bindiga, su ka kuma kashe su. Kawo yanzu dai, jami’an tsaro na cigaba da yin sintiri a jiragen yaki domin ganin an samar da zaman lafiya a a jihar Zamfara.