Jami’ar al Qalam da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya ta musanta labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an kai harin ban makarantar, tana cewa wannan “abin takaici” ne yada irin wadannan labaran karyar.”
Wannan kunshe ne cikin wata sanawrwa da shugaban hulda da jama’a na jami’ar Akilu A Atiku ya fitar.
“Abin da ya faru wata tayar babbar mota ce da ke tafiya ta fashe a kan titin Dutsinma da misalin karfe 8:30 na yamma amma wasu marassa kishi suke yada labarin cewa wai harin bam aka kai wa jami’ar.”
Al Qalam ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labari ba gaskiya ba ne.