Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Taraba

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Taraba

84
0

Hankula sun tashi a kauyen Jauro Manu na karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba, sakamakon kashe mutane biyar da ‘yan bindiga suka yi, sannan kuma ‘yan bindigar sun yi barazanar kai hari a wasu karin garuruwa da ke yankin.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa maharan, kimanin su shida sun kai farmaki garin Jauro Manu, Sannan suka kashe wani mutum mai suna Musa Iraniya, dan kasuwa kuma manomi.
Ya kara da cewa sabon barazanar da ‘yan bindigar suka yi, ya jefa jama’a cikin tsoro yayin da mazauna garin suke tunanin tserewa zuwa Mutum-Biyu, shelkwatar karamar hukumar.
Musa Yakubu, wani mazaunin garin ya fadawa manema labarai cewa ba a taba kai hari garin ba sai a sabuwar shekarar nan.