Home Home Zaben 2023: Jonathan Ya Yi Zaman Sirri Da Masu So Ya Koma...

Zaben 2023: Jonathan Ya Yi Zaman Sirri Da Masu So Ya Koma Kan Mulki

137
0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, ya gana da jagororin kudu maso kudu da suke sha’awar ganin ya koma kan mulki a 2023.

Wasu rahotanni a ranar 27 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, sun bayyana cewar tsohon shugaban kasa ya hadu da masu son ganin ya koma mulki.
Wata majiya ta ce bayan wannan zama da aka yi ne aka ga Jonathan ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar sa dake Abuja.
Sai dai zuwa yanzun ba a bayyana asalin abinda suka tattauna ba.

Leave a Reply