Home Home Martani: Ohanaeze Ta Ce Dole Jonathan Ya Goyi Bayan Takarar Ɗan Kaɓilar...

Martani: Ohanaeze Ta Ce Dole Jonathan Ya Goyi Bayan Takarar Ɗan Kaɓilar Igbo A 2023

570
0

Ƙungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta ce ya kamata tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya goyi bayan ganin tabbatar da an zaɓi ɗan ƙabilar a matsayin shugaban ƙasa a 2023.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar Alex Ogbonna ya ce halin da Ndigbo ke ciki zamanin mulkin shugaba Buhari saboda goyon bayan da ƴan kaɓilar Igbo suka ba Jonathan ne.
Ogbonna, ya yi tsokaci ne kan rahotannin cewa tsohon shugaba Jonathan ya gana da shugabannin kudu maso kudu ya na neman goyon bayansu domin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.
Ya tabbatar da cewar su tunanin su tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai goyi bayan Igbo, domin a rama wa kura aniyar ta.

Leave a Reply