Home Labarai Sojojin Najeriya Sun Ƙashe Ƴan Ta’adda 2245 Cikin Wata Uku

Sojojin Najeriya Sun Ƙashe Ƴan Ta’adda 2245 Cikin Wata Uku

271
0
Chief of Defence Staff Gen. Christopher Musa
Chief of Defence Staff Gen. Christopher Musa

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun ta sun kashe ‘yan ta’adda 2245 cikin wata uku na biyun shekara.

Rundunar sojojin Najeriya ta kuma bayyana kama akalla mutum 3,682 da ake zargi da ayyukan ta’addanci da sauran laifuka,

tare da kubutar da mutumane da aka yi garkuwa da su yayin wasu samame a sassan ƙasa cikin watannin.

Darakta yada labarai na Ma’aikatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai

a shelkwatar tsaro dake Abuja, ya kuma ce sojojin sun kwato makamai 2,783 da alburusai 64,547.

Buba, ya kuma bayyana cewa, sojojin Najeriya ƙarƙashin  “Operation Delta Safe”,

sun kuma ɗakile yunkurin barayin ɗanyen mai kan satar man da aka kiyasta ya haura Naira biliyan 10.

Leave a Reply