Mayakan Boko Haram uku sun mika wuya ga sojojin hadin gwiwa da ke fatattakar masu tayar da zaune tsaye.
sanarwa da kakakin rundunar da ke yakar Boko Haram a Kamaru da Najeriya da Chadi, Leftanat Kanar Abubakar Abdullahi
ya ce mayakan Boko Haram biyu ne suka mika wuya ga sojoji a yankin Wulgo da ke Kamaru.
A cewar sanarwar, runduna ta uku a Najeriya ta bayar da rahoton dan Boko Haram guda ya mika wuya a yankin Baga,
Binciken ya nuna cewa mutumin ya shafe shekara shida zaune a yankin Kwaleram da ke tafkin Chadi a matsayin dan kungiyar Boko Haram.