Home Labarai Barayin Daji: Mutum 143 Da Ake Zargi Sun Shiga Hannu A Kaduna

Barayin Daji: Mutum 143 Da Ake Zargi Sun Shiga Hannu A Kaduna

210
0
7A87163D D292 41E4 8DD4 8280F2980816
7A87163D D292 41E4 8DD4 8280F2980816

‘yan sanda jihar sun tabbatar da kamen mutum 143 da ake zargi masu satar mutane ne da kuma yan fashi

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a shelkwatar rundunar

inda ya ce an gano wasu manyan makamai daga hannun mutanen.

Mutanen da aka kama sun hada da yan fashi 73 sai ‘yan bindiga 70 ciki har da wanda ake nema ruwa a jallo,

da aka damke a lokacin da yake kokarin hada wa ‘yan bindigar wani tsubbu domin gudanar da ayyukan su.

Ya kara da cewa ‘yan sandan sun halaka ‘yan bindiga tara cikin wata biyu da suka gabata.

cikin makaman da aka gano hannun mutanen da ake zargi sun hada da bindiga kirar AK47 da alburusai da dama.

Ya kara da cewa an sake kama mutum 985 da ake zargi masu satar waya ne da yan fashi takawas,

da kuma wani da ake zargi da satar kaya a tashar jirgin kasa.

Leave a Reply