Home Labaru Siyasar Rivers: Hukumar Zabe Ta Cigaba Da Tattara Kuri’un Zaben Gwamna

Siyasar Rivers: Hukumar Zabe Ta Cigaba Da Tattara Kuri’un Zaben Gwamna

378
0

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta kori karar da jam’iyyar AAC ta shigar domin a hana ci-gaba da tattara kuri’un Zaben gwamna a Jihar Rivers.

Kotun ta ce babu wata hujjar da jam’iyyar za ta kafa da har za ta nemi a tsaida ci-gaba da zaben da dokar kasa ce ta bada iznin gudanar da shi.

Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ce tunda abin da ake tankiya a kai ya faru a baya kuma an shiga lokaci na bayan zabe, to Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ce ta cancanta ta saurari karar ba Babbar Kotun Tarayya ba.Tuni dai hukumar zabe ta cigaba da tattara sakamakon zaben, wanda ta ce bayan kammala tattarawa ne za a bayyana wanda ya yi nasara.

Leave a Reply