Home Labaru Shari’ar Zabe: Kotu Ta Kwace Kujerar PDP A Majalisar Wakilai Ta Ba...

Shari’ar Zabe: Kotu Ta Kwace Kujerar PDP A Majalisar Wakilai Ta Ba Jam’iyyar APC

328
0

Kotun sauraren kararrakin zabe da ke zama a birnin Akure na jihar Ondo, ta soke zaben Ikebgboju Gboluga, a matsayin dan majalisar wakilai daga mazabar Okitipupa da Irele a karkashin jam’iyyar PDP.

An dai soke zaben Gboluga ne, bisa dalilin cewa ba ya da hurumin yin takara a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019, saboda mallakar takardun zama dan asalin kasar Ingila tare da yin rantsuwar zama mai biyayya ga kasar kafin a ba shi takardun shaidar zama dan kasa.

Kotun, ta bayyana sunan Albert Akintoye na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben, tare da ba hukumar zabe ta kasa umarnin ta karbe shaidar cin zabe daga hannun Gboluga ta ba Akintoye.