Home Labaru Zaman Kashe-Wando: Matawalle Zai Dauki Sabbin Ma’aikata 8000 A Jihar Zamfara

Zaman Kashe-Wando: Matawalle Zai Dauki Sabbin Ma’aikata 8000 A Jihar Zamfara

913
0

Gwamnan jihar Zamfara Dakta Bello Matawalle Maradun, ya ce gwamnatin sa ta kammala shiri daukan sabbin ma’aikata 8000 a fadin jihar, ya na mai cewa tuni gwamnatin sa ta tara kudaden da za ta rika biyan sabbin ma’aikatan albashin su.

Ya ce sabbin ma’aikatan da za su dauka, bai hada da matasa dubu 1 da 400 da gwamnatin da ta gabata ta dauka ta kasa biyan su har na tsawon shekaru 2 ba.

Matawalle ya kara da cewa, gwamnati ta ware naira Miliyan 150 domin tallafa wa mata dubu 7 da 500 a fadin jihar, sannan za su zabi mata dubu 1 da 500 su rika biyan su naira 20,000 a kowane wata domin inganta sana’o’in su.

A karshe ya ce sun samu tallafin tireloli 50 na takin zamani daga gwamnatin tarayya domin amfanin manoman jihar, ya na mai tabbatar da cewa gwamnatin sa ta jama’a ce, kuma za su tabbatar da an ciyar da jihar Zamfara gaba kamar yadda su ka daura damarar aiwatarwa.