Home Labaru Rikici: Mutane 11 Sun Mutu A Taraba Da Benue Sakamakon Rikicin Kabilanci

Rikici: Mutane 11 Sun Mutu A Taraba Da Benue Sakamakon Rikicin Kabilanci

431
0

Matasa a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba, sun kashe akalla mutane takwas a wani harin daukar fansa a kan wani mutumin Jukun da aka kashe a gonar sa da ke hanyar Takum zuwa Wukari.

Har ila yau, mutane uku sun rasa rayukan su a wani mumunan rikici da ya barke tsakanin matasan Edumoga da Okpoga da ke karamar hukumar Okpokwu a jihar Banue.

Yayin da ya ke tabbatar da lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Taraba DSP David Misal, ya ce mutane biyu ne aka kashe, amma a halin yanzu an shawo kan matsalar.

Game da sabon rikici da ya barke tsakanin matasan Edumoga da Okpoga a karamar hukumar Okpokwu ta jihar Benue, rahotanni sun ce rikici tsakanin kauyen Ollo a yankin Edumoga da sassan Okpoga ya sake tasowa ne a daren ranar Litinin da ta gabata, yayin da matasan Ollo su ka kai hare-hare a yankunan Okpoga.

Sai dai a lokacin da aka tuntube ta, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue DSP Catherine Anene, ta ce ba ta samu bayanai a kan rikicin ba tukunna.

Leave a Reply