Home Home Sarkin Musulmi Ya Ce A Duba Jinjirin Watan Ramadan A Ranar Laraba

Sarkin Musulmi Ya Ce A Duba Jinjirin Watan Ramadan A Ranar Laraba

16
0
Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci Musulmin Nijeriya su fara duban jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Larabar nan.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci Musulmin Nijeriya su fara duban jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Larabar nan.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan tafiyar da harkokin majalisar harkokin addinin musulunci ta Nijeriya Zubairu Haruna Usman Ugwu ya fitar.

Sanarwar, ta ce an yanke shawarar haka ne a wani zama da kwamitin duban wata ya yi, inda shugaban kwamitin ya bukaci Musulmi su tuna cewa, ranar Laraba ce 29 ga watan Sha’aban na shekara ta1444 bayan Hijira.

Ranar Laraba dai za ta yi daidai da 22 ga watan Maris na shekara ta 2023 Miladiyya.