
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar Jam’iyyar APC Dakta Nasir Yusuf Gawuna, ya ce hukumar zabe ta yi kuskure wajen bayyana Abba Kabir na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar sakamakon soke zaben wasu mazabun da aka yi.
Yayin ganawa da manema labarai, Gawuna ya ce yawan akwatunan da aka soke ya kai a ce hukumar zabe ta sake gudanar da zabubbuka a wuraren kafin gabatar da kammalallen sakamako da kuma sanar da wanda ya ci.
Gawuna, ya ce duba da yadda hukumar zaben ta bayyana zaben ‘yan majalisun jihar Kano 16 a matsayin wadanda ba su kammala ba, ya dace a ce ta dauki irin wannan matakin a zaben kujerar gwamna.
Ya ce suna da yakinin cewa Allah ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so, don haka za su bi matakan da su ka dace ta fannin shari’a domin neman hakkin su.
You must log in to post a comment.