Home Home Lokaci Ya Yi Da Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa – Kalu

Lokaci Ya Yi Da Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa – Kalu

11
0

Mai tsawatarwa na majalisar dattawa Orji Kalu ya ce lokaci ya yi da zai zama shugaban majalisar.

Yayin da ya ke magana da manema labarai a harabar majalisar, Orji Kalu ya buƙaci jam’iyyar APC ta ware wa yankin sa kujerar shugaban majalisar dattawa.

Orji Kalu, ya ce shi ne sanata mafi girman matsayi daga yankin kudu maso gabashin Nijeriya, don haka shi ne ya dace da muƙamin.

Kawo yanzu dai, jam’iyyar APC ba ta sanar da shiyyoyin da za ta ware wa muƙaman shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai ba.