Home Home Sarkin Lafiya Sidi Bage Ya Bukaci Daukar Matakin Dakile Yunwa A Najeriya

Sarkin Lafiya Sidi Bage Ya Bukaci Daukar Matakin Dakile Yunwa A Najeriya

149
0

Mai martaba Sarkin Lafiya Sidi Mohammed Bage, ya koka a kan halin kuncin rayuwar da jama’a ke ciki, inda ya bukaci gwamnati da ‘yan kasuwa su dauki matakin saukaka wa al’umma.

Basaraken ya ce, bayan shirin gwamnati na ba jama’a kayan masarufi a matsayin tallafi, su ma ‘yan kasuwa su na da rawar da za su taka wajen rage wa jama’a radadin halin da ake ciki, ta fuskar rage farashin kayan abinci domin ganin talakawa sun samu abin da za su ciyar da iyalan su.

Sarki Bage, ya ce tallafin man fetur da gwamnatin shugaba  Tinubu ta cire ba abu ne mai sauki a wannan lokacin ba, amma ana bukatar matakan tattalin arziki masu ingancin da za su taimaka wa jama’a wajen rage masu radadin halin kuncin da su ka samu kan su a yanzu.

Basaraken, ya kuma bukaci ‘yan kasuwa a fadin Nijeriya su taimaka wa gwamnati duk inda su ke, wajen ganin an shawo kan wannan matsala ta tsadar kayan abinci da ta mamaye kasa.

Leave a Reply