Majalisar Dattawa Ta Kafa Kwamiti Mai Mutane 45 Da Za Su Yi Aikin Gyaran Fuska Ga Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Na Shekara Ta 1999.
Shugaban Majalisar Godswill Akpabio Ya Sanar Da Kafa Kwamitin A Ranar Laraba, Tare Da Cewa Za A Kaddamar ‘Ya’yan Kwamitin A Ranar Talata Mai Zawa, Kuma Nan Take Za Su Fara Aiki.
Akpabio Bayyana Cewa, Kundin Tsarin Mulki Na Shekara Ta 1999 Na Bukatar Sake Duba Shi, Saboda A Cikinsa Akwai Batutuwa Da Dama Da Ya Kamata A Gyara Su.
Ya Ce Kwamitin Na Da Wakilcin Sanata Daya Daga Kowace Jiha Da Kuma Birnin Abuja, Sai Kuma Wakili Daya Daga Kowace Shiyyar Nijeriya.
Haka Kuma, Akpabio Ya Bukaci A Gabatar Da Shawarwari Da Bangororin Kundin Tsarin Mulkin Ke Bukatar A Yi Wa Kwaskwarima, Sannan Ya Umarci Kwamitin Ya Gayyaci Shugaban Majalisar Dokokin Kowace Jiha Domin Tattaunawa Da Kuma Bada Gudummawa.