Gwamnatin tarayya ta ce za ta cigaba da biyan tallafin Naira dubu 35 da ta fara biyan ma’aikata domin rage radadin illar cire tallafin man fetur ga ma’aikata.
Haka kuma, Gwamnatin ta roki kungiyoyin kwadago na Nijeriya su janye yajin aikin da su ka shirya yi na tsawon kwanaki 14.
Karamar ministar Kwadago Nkeiruka Onyejeocha ta bada wannan tabbacin a Abuja, a wajen wani taro da shugabannin ƙungiyoyin kwadago da aka yi a kan wa’adin da su ka ba gwamnati na tafiya yajin aiki idan ba ta biya masu bukatun su ba cikin makonni biyu.
An dai cimma yarjejeniyar ne a ranar 2 ga watan Oktoba na shekara ta 2023 mai dauke da abubuwa 16, wadanda su ka hada da ƙarancin albashin ma’aikata da tallafin naira dubu 35 ga ma’aikata duk wata da dai sauran su.
Ministar ta yi nuni da cewa, yayin da martanin kungiyoyin kwadagon a kan gazawar gwamnati na cika yarjejeniyar bai dace ba, ya na da kyau a yi la’akari da cewa wasu abubuwa da ke cikin yarjejeniyar ba za a iya cimma su ba a lokaci guda.