Home Labaru Samar Da Abin Yi: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Daukar Tsofaffin Sojoji Da...

Samar Da Abin Yi: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Daukar Tsofaffin Sojoji Da Iyalan Su Aiki

550
0

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin daukar tsofaffin sojoji aiki tare da iyalan su da ma sauran  jama’a ga duk mai sha’awa.

Wata majiya daga hukumar tsaro ta sojoji ya shaida wa manema labarai cewa, an amince da fara daukar su ne a cikin wannan makon.

An dai kafa wasu jami’ai na daukar tsofaffin sojojin masu bukatar karin kudaden shiga baya ga fanshon da su ke karba duk wata.

Tuni dai an umarci mahukuntan sojin kasa da na sama da na ruwa su rarraba takardun neman aiki a duk ofisoshi da barikokin su a fadin Nijeriya, domin a dauki jami’an da su ka yi ritaya.

An dai kirkiro shirin ne, domin a samu hanyoyin rage radadin rashin aiki, wanda ya kara muni sosai a cikin shekaru hudu sakamakon yawan korar ma’aikata.