Home Labaru Rai Dangin Goro: Majalisar Dattawa Ta Tafi Hutun Makonni Takwas

Rai Dangin Goro: Majalisar Dattawa Ta Tafi Hutun Makonni Takwas

310
0

Bayan bayyana sunayen shugabanni da ‘yan majalisar dattawa da Sanata Ahmed Lawan ya yi a Zauren majalisar, ya ce majalisar za ta tafi hutun ta na shekara-shekara na tsawon makonni takwas.

Kafin rufe majalisar, Shugaban majalisar ya yaba wa sanatoci bisa kokarin da su ka yi na jurewa har aka kammala tantance ministocin da shugaba Mauhammadu Buhari ya aike masu.

Sanata Ahmed Lawan ya bada tabbacin cewa, wannan shi ne karo na farko da majalisa ta yi namijin kokari wajen ganin tun da ta fara aikin tantance ministoci sai da ta kai karshe.

Ya ce sun dakatar da hutun su don ganin an kammala aikin, ya na mai rokon wadanda za a nada su kwana da shirin cewa za su yi aiki ne tare domin ci-gaban kasa, sannan  majalisar za ta rika bibiyar ayyukan su don tabbatar da an yi abin da ya dace.