Home Labaru Tantance Ministoci: Shugaba Buhari Ya Yaba Wa Majalisar Dattawa

Tantance Ministoci: Shugaba Buhari Ya Yaba Wa Majalisar Dattawa

244
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba wa majalisar dattawa bisa yadda su ka gaggauta tantance sunayen ministocin da ya aike masu a makon da ya gabata.

‘Yan majalisar dai sun kammala tantance ministocin 43 ne a cikin kwanaki biyar.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, Buhari ya ce ya na fatan kafa majalisar zartarwa nan ba da jimawa ba, lamarin da ke nufin zai rarraba ma’aikatu ga zababbun ministocin da aka tantance.

Ya ce ya gamsu da yadda majalisar dattawa ta amince da ministocin da ya aike mata, ta yadda su ka gaggauta aikin tantancewar.