Home Labaru Sakon Sallah: Mutane Na Shan Bakar Wahala-Sarkin Zazzau

Sakon Sallah: Mutane Na Shan Bakar Wahala-Sarkin Zazzau

1124
0

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris, ya yi kira ga shugabanni tun daga matakin jahohi zuwa tarayya su samarwa jama’a saukin rayuwa domin fita daga kangin rayuwa da suka fada.

Sarkin Zazzau, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na barka da Sallah a fadarsa dake birnin Zazzau, inda ya nemi gwamnatoci a dukkanin matakai su jajirce wajen kula da walwalar ‘yan Najeriya.

Ya ce ya kamata gwamnatoci su waiwayi ‘yan Najeriya su tallafa musu wajen fita daga cikin bakar wahalar da suke fama da shi.

Mai martaba sarkin zazzau ya yi kira ga alumma su daure wajen zaman lafiya da junan su, sannan kuma makiyaya da manoma su girmama juna, su daina yada jita-jita kuma su ba jami’an tsaro hadin kai.

Ya ce gwamnatin jahar Kaduna da ta kananan hukumomi da majalisar dokokin jiha su dauki matakan samar da ci gaba ta bangaren noma da kiwo da kuma ilimi, ya ce idan aka samar da wadannan abubuwa, za a sami da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Haka zalika, Sarkin ya yi kira ga gwamnati da ta taimakawa manoma wajen sayen amfanin gonarsu domin su samu riba, sannan ya yi kira ga jama’a su gaggauta sanar da hukuma wanzuwar duk wasu cututtuka a yankunan su.