Home Labaru Kasar Saudiyya: Wani ‘Dan Najeriya Ya Dawo Da Dala Dari 800...

Kasar Saudiyya: Wani ‘Dan Najeriya Ya Dawo Da Dala Dari 800 Da Ya Tsinta

348
0

Wani mahajjacin Najeriya wanda ke gudanar da aikin hajji a kasar Saudiyya, ya tsinci wasu makudan kudade da yawansu ya kai dala dari 8, amma ya mayar da su ga jami’an hukumar aikin hajji.

Mahajjacin mai suna Suleman, wanda shi ne direban sarkin Keffi na jihar Nasarawa, ya dawo da kudin ga hukumar aikin hajji na jihar Nasarawa a kasar Saudiyya.

Amirl hajji kuma sarkin Lafia, Sidi Dauda Bage, ya karrama mahajjacin akan aikin alkhairi da ya yi, inda ya yi godiya akan aikin alkhairi da karamcin da ya nuna.

Sarkin Lafia, Sidi Dauda Bage, ya bukaci alummarsa su kasance masu aikin alkhairi a duk inda suka tsinci kansu, saboda cuta ba ta  da wani amfani.