Home Labaru 2023: Yankin Arewa Za Ta Zama Butulu Idan Har Bata Mika Wa...

2023: Yankin Arewa Za Ta Zama Butulu Idan Har Bata Mika Wa Kudu Mulki Ba – Shehu Sani

379
0

Tsohon dan majalisar dattawa Shehu Sani, ya nuna rashin jin dadin sa akan wadanda ke da muradin ganin arewacin Najeriya  ta rike mulki fiye da shekara ta  2023.

Shehu Sani, ya ce arewa za ta zama butulu idan har taki mika mulki ga yankin kudu idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa na biyu.

Tsohon dan majalisar na mayar da martani ne, akan kira da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi kan soke batun mulkin karba-karba.

Shehu Sani, ya ce zai zama rashin adalci ga arewa idan ta ci gaba da rikon mulkin Najeriya bayan shekaru 8.

Shehu Sani, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar Sallah ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa, inda ya ce yankin kudu, musamman kudu maso yamma, sun yi duk kokarin su domin ganin Buhari ya yi nasara a zaben 2015.

Shehu Sani tare da tsohon gwamnan jihar Kaduna Balarabe Musa

Gwamna El-Rufai ya nemi a daina rabon mukaman siyasa ga yankuna, ya ce  akwai bukatar sake duba lamarin da kuma soke rabon domin a ba da damar duba kokarin mutum.

Ya ce ba zai yiwu Najeriya ta ci gaba akan wannan turba ba, na rabon mukamai zuwa ga yanki ko asali ba, inda ya bayyana hakan a matsayin shinge ga daidaituwar siyasar Najeriya.