Home Labaru Sakamakon Zabe: Hukumar Zabe Ta Karyata Atiku Abubakar A Gaban Kotu

Sakamakon Zabe: Hukumar Zabe Ta Karyata Atiku Abubakar A Gaban Kotu

332
0
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta zargi dan takarar shugabann kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, da kirkirar wa kan sa sakamakon zabe na bogi, domin kafa hujja da shi a gaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa.

Wannan ya na daga cikin martanin da hukumar ta yi wa Atiku a kotu, inda ta ce babu wani rumbu na na’ura da ta tattara sakamakon zaben shekara ta 2019, ballantana har Atiku ya yi ikirarin ganin abin da ke ciki har ya kwafo ya nuna.

Lauyan hukumar zabe Yunus Usman, ya ce ko kusa ba a tattara sakamakon zaben shugaban kasa ko watsa shi a na’urorin sadarwa ba.

Hukumar zaben ta kara da cewa, babu wani rumbun na’urar da ta tattara ko ta killace sakamakon zaben a ciki, ballantana har Atiku ya shiga ya leko sakamakon da ya yi ikirarin cewa shi ya samu.

Atiku dai ya yi ikirarin cewa, kuri’u miliyan 18 da dubu 356 da 732 ya samu, yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu miliyan 16 da dubu 741 da 430.

Leave a Reply