Home Labaru Ilimi Kasafin Ilimi: ASUU Ta Kalubalanci Gwamnatin Tarayya

Kasafin Ilimi: ASUU Ta Kalubalanci Gwamnatin Tarayya

307
0
Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Nijeriya ASUU
Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Nijeriya ASUU

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU, ta bayyana damuwa, tare da rashin gamsuwar a kan tanadin da gwamnatin tarayya ta yi wa sashen ilimi a cikin kasafin bana.

Yayin bayyana rashin gamsuwar ta a kan tanadin, kungiyar ta  kuma ce gwamnati ta yaudare ta sakamakon rashin tabbatar da yarjejeniyar da su ka yi a watan Fabrairun da ya gabata.

Kamar yadda kungiyar ta bayyana, gwamnatin tarayya ba ta biya naira biliyan 25 na hakkokin malaman jami’o’i da ta amince za ta biya gabanin janye yajin aikin ta watanni biyu da su ka gabata.

Farfesa Omole, ya ce gwamnatin tarayya ta ingiza kungiyar Malaman wajen amincewa da alkawurran ta da a halin yanzu tanadin da ta yi wa sashen ilimi a Nijeriya ya tabbatar da rashin amincin ta.

Leave a Reply