Home Labaru Difilomasiyya: Shugaba Buhari Ya Taya Netanyahu Murnar Sake Lashe Zabe

Difilomasiyya: Shugaba Buhari Ya Taya Netanyahu Murnar Sake Lashe Zabe

185
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya takwaran sa Firayin Minista Benjamin Netanyahu na Isra’ila murnar sake lashe zaben da aka gudanar a kasar.

Netanyahu dai zai cigaba da zama Shugaban kasar Isra’ila, bayan jam’iyyar su ta gamayya ta yi nasarar lashe zaben da aka gudanar.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya yi fatan alheri ga daukacin al’ummar kasar Isra’ila, bayan samun gagarumar nasarar kammala zabe, tare da yi masu fatan samun zaman lafiya da ci-gaba.

Ya ce Shugaba Buhari ya na son gani da fatan ci-gaba da aiki kafada-da-kafada da Shugaban Isra’ila, domin karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.