Ɗan ƙwallon Jamus, Ikay Gundogan ya sake komawa Manchester City, inda ya saka hannu a kwantiragin shekara guda.
Ɗan wasan ya dawo ƙungiyar, da ke riƙe da kofin Premier , kimanin wata 12 baya barin ƙungiyar.
Gundogan ya kwashe shekara bakwai a Manchester City, inda ya lashe kofuna da dama, har ya kai ga zama kyaftin ɗin ƙungiyar.
Ya kwatanta lokacin sa a Manchester City a matsayin lokacin farin ciki, sannan ya ce ya ƙagu ya ci gaba taka leda a ƙungiyar.
Gundogan na cikin ƴan wasan da suka fi ɗaukar albashi a Barcelona, wanda tafiyar sa zai taimaka wa ƙungiyar wajen daidaita kashe kuɗin su domin gudun karya doka.














































