Home Labaru Yawan ‘Yan Wasa: Kocin Chelsea Ya Ce Ba Za Ta Taɓuka Abin...

Yawan ‘Yan Wasa: Kocin Chelsea Ya Ce Ba Za Ta Taɓuka Abin Kirki Ba

368
0
bbbec2d0 614a 11ef b970 9f202720b57a
bbbec2d0 614a 11ef b970 9f202720b57a

Maresca ya ce za a iya samun matsaloli idan kulob ɗin bai iya rage yawan manyan ƴan wasansa ba kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan wasa.

Blues ta ɗauko ƴan wasa 11 a wannan bazarar wanda ya sa adadin manyan ƴan wasan ƙungiyar ya kai sama da 40.

A farkon makon nan, Maresca ya ce ƴan wasan Ingila Raheem Sterling da Ben Chilwell na cikin rukunin ƴan wasa kusan 15 da aka ce su yi atisaye da tawagar matasan ƙungiyar.

Kocin ya ce babu wani koci a duniya da zai iya aiki tare da ƴan wasa 45 dan ba abu ne mai yiwuwa ba, ba za a iya yin hakan ba.

Leave a Reply