Wasu motoci maƙare da kayan agaji sun sami nasarar ratsa iyakar Adre zuwa yankin Darfur na Sudan da yunwa ta yiwa lahani,
matakin da ke biyo bayan ɗage haramcin shigar da kayan da sojoji suka yi.
Iyakar Adre ta Chadi itace mafi kusa da isa Darfur, kuma sojoji da kuma abokan rikicin na su da mayakan RSF sun hana shigar da kayan agaji cikin wata 16 da aka kwashe ana tafaka yakin.
A wata Fabrarun da ya gabata ne gwamnatin sojin ƙasar ta bada umarnin dakatar da shigar da kayan agaji ta wannan mashigin a hukumance, tana mai cewa dakarun na RSF na samun makamai ta wannan iyaka.
Hukumar bada agajin gaggawa ta majalisar ɗinkin duniya a Sudan ta bakin shugabanta Justin Brady ta ce zuwa yanzu manyan motoci 15 ne suka isa yankin na Darfur cikin guda 131 da ke kan iyakar suna jiran umarnin shiga.
A wata sanarwa da hukumar samar da abinci ta majalisar ɗinkin duniya ta fitar ta ce kayan abincin da suka sami damar shiga yankin sun haɗa da man girki, da shinkafa, da Dawa, da sauran su, kuma ana sa ran za su ishi mutane dubu 13.
Hukumar ta ce tana fatan sojojin zasu bada damar shigar da dukannin kayan abincin da ta tanada wadanda za su ishi mutane akalla dubu 500.














































