‘Yan majalisar wakilai sun saurari ra’ayin jama’a a kan yiwuwar yin kudurin doka da nufin ba Jakuna kariya daga safarar su da ake yi zuwa kasashen ketare.
A ranar Talatar da ta gabata, majalisar wakilai ta saurari ra’ayin jama’a karo na biyu, inda take shirin gabatar da shi domin zama kudurin doka, musamman game da barazanar karewa da Jakuna ke fuskanta sakamakon safarar su ba bisa ka’ida ba.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwadabawa da Illela a jihar Sokoto Abdullahi Balarabe Salame ya shaida wa manema labarai cewa, al’amarin ya dade ya na ci wa ‘yan Nijeriya tuwo a kwarya, musamman a yankunan karkara da su ka fi amfani da jakuna a matsayin abin sufuri.‘Yan majalisar, su na fatan da zarar an amince da dokar an kuma fara aiki da ita, za a fitar da jadawalin yadda za ta kasance da hukuncin da aka tanadar ga wanda duk ya taka ta.