Home Labaru Kudin Maraba: Za A Kashe Wa Zababbun ‘Yan Majalisun Dokoki Naira Biliyan...

Kudin Maraba: Za A Kashe Wa Zababbun ‘Yan Majalisun Dokoki Naira Biliyan 4,068,000,000

340
0
Majalisar Dattawa

Kimanin naira biliyan hudu da miliyan sittin da takwas ne za a rarraba wa zababbun ‘yan majalisun dokoki na tarayya a matsayin kudin maraba da zarar an rantsar da su a watan Yuni na shekara ta 2019.

Bincike ya nuna cewa, ana biyan duk wani sabon dan majalisa wadannan kudaden ne domin ya samu wurin zama da na kayan daki.

Bayanai daga hukumar rarraba arzikin kasa ya nuna cewa, ana biyan ‘yan majalisu kudin wurin zama sau daya ne a duk shekara, yayin da ake biyan su alawus na kudin kayan daki sau daya a shekara.

Kudin da dokokin hukumar na shekara ta 2007 su ka tanadar a biya duk wani majalisar wakilai na alawus shi ne naira miliyan tara da dubu dari tara da ashirin da shida da sittin da biyu da kwabo 5.Binciken ya cigaba da cewa, dokar ta tanadi a biya dan majalisar dattawa naira miliyan goma da dubu dari da talatin da biyu a matsayin kudin gida da na sayen kayan daki.

Leave a Reply