Home Labaru Takaddama: INEC Ta Janye Shahadar Zaben Kawu Sumaila Ta Ba Dan Minista...

Takaddama: INEC Ta Janye Shahadar Zaben Kawu Sumaila Ta Ba Dan Minista Dambazau

731
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta Kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta kwace shahadar nasarar zabe daga hannun Sulaiman Kawu Sumaila ta damka wa Shamsuddeen Abdurrahman Dmabazau.

Da farko dai hukumar ta damka shaidar ne ga Kawu Sumaila, amma Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta soke takarar shi bisa dalilin cewa ba bisa ka’ida ya fito takara ba.

Dambazau ya garzaya kotu, inda ya kalubalanci Kawu Sumaila a matsayin dan takarar APC, bisa dalilin cewa Sumaila bai tsaya takara a zaben fidda gwanin APC na dan majalisa daga mazabar Takai da Sumaila ba. Da farko dai Kawu Sumaila ya fito takarar Sanata ne, amma Kabiru Gaya ya kada shi a zaben fidda-gwani.