Home Labaru Labarun Ketare Sabuwar Dokar Zabe A Bolivia Ta Haramta Wa Morales Yin Takara

Sabuwar Dokar Zabe A Bolivia Ta Haramta Wa Morales Yin Takara

272
0
Sabuwar Dokar Zabe A Bolivia Ta Haramta Wa Morales Yin Takara
Sabuwar Dokar Zabe A Bolivia Ta Haramta Wa Morales Yin Takara

Majalisar dokoki ta kasar Bolivia, ta amince da wani kudirin dokar zabe da zai ba da damar gudanar da zabubbuka ba tare da tsohon shugaba Evo Morales ba, yayin da gwamnatin wucin-gadin kasar ke tattaunawa da masu zanga-zanga don kawo karshen tarzomar da aka shafe makonni ana yi.

Akalla mutane 32 ne su ka mutu a tarzomar da ta tashi, biyo bayan takaddamar da ta kunno kai a kan sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 20 ga watan Oktoba, lamarin da ya janyo karancin abinci da man fetur a birnin La Paza da sauran birane.

Dukkan majalisun biyu sun kada kuri’ar goyon baya ga kudirin da za a mika wa shugabar rikon kwarya Jeanine Anez, wadda za ta sa hannu ya zama doka.

Dokar, ta kuma soke sakamakon zabubbukan da aka gudanar ranar 20 ga watan Oktoba, sannan ta bada damar gudanar da wasu zabubbukan nan gaba.

Haka kuma, ta haramta wa ‘yan takarar da su ka yi aiki a gwamnatin da ta shude sake tsayawa takarar neman mukamin da su ka taba rikewa.

Leave a Reply