Home Labaru Wata Babbar Mota Ta Take Jami’in Karota A Kano

Wata Babbar Mota Ta Take Jami’in Karota A Kano

529
0
Wata Babbar Mota Ta Take Jami’in Karota A Kano
Wata Babbar Mota Ta Take Jami’in Karota A Kano

Hukumar kula da cunkuson ababen hawa a jihar Kano KAROTA, ta kara yin rashin wani jami’in ta da yammacin ranar Asabar da ta gabata, sakamakon take shi da wata babbar mota ta yi kusa shatale-talen gidan man fetur na NNPC da ke unguwar Hotoro.

Mutuwar jami’in dai ta na zuwa ne, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta sanar da cewa, ta yi nasaar kama wani direban mota da ya tsere bayan ya take wani jami’in KAROTA mai suna Ahmad Tijjani a ranar 29 ga watan Oktoba.

Direban dai ya buge Tijjani ne, yayin da ya ke kokarin kwance masa lambar mota sannan ya tsere, amma ranar Juma’a da ta gabata rundunar ‘yan sanda ta sanar da kama shi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar KAROTA Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa, ya ce jama’ar da abin ya faru a kan idon su ne su ka kama direban babban motar, sannan su ka damka shi a hannun jami’an ‘yan sanda yayin da ya ke kokarin gudu bayan ya take jami’in na KAROTA.

Leave a Reply