Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya, ya ce suna fuskantar matsalloli wajen kai dauki ga ‘yan gudun hijira da ke wasu yankunan kasar Burkina Faso.
Kungiyar ‘yan gudun hijira da abokan huldar su dai su na fama da barrazana daga kungiyoyin ‘yan ta’adda, wanda hakan ya ke a matsayin babbar matsala ga wadanan kungiyoyi.
Kakkakin
kungiyar Babar Baloch da ke magana a birnin Geneva, ya ce akalla mabukata dubu
dari biyar ne yanzu haka su ke bukatar a kai masu dauki, wasu daga cikin su
rikicin ya tilasata masu barin gidanjen su ba tare da sun shirya ba.














































