Home Labaru Rushe Masallacin: Asari Dokubo Ya Kalubalanci Gwamnan Rivers

Rushe Masallacin: Asari Dokubo Ya Kalubalanci Gwamnan Rivers

767
0
Asari Dokubo Ya Kalubalanci Gwamnan Jihar Rivers
Asari Dokubo Ya Kalubalanci Gwamnan Jihar Rivers

Shugaban kungiyar yankin Niger Delta Asari Dokubo, ya karyata gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a game da maganar ruguza wani masallaci a jihar.

Karanta Wannan: Kanjamau: Za A Rika Karbar Magani Kyauta A Jihar Rivers – Wike

Dokubo, ya bayyana cewa babu shakka Nyesom Wike ya rusa wannan babban masallaci na Trans-Amadi da ake magana da ke cikin a Fatakwal.

Ya ce gwamnatin jihar Rivers  ta na ikirarin cewa ba ta ruguza wani masallaci ba, amma a wani bidiyo da ke yawo a kafafen zamani, an nuna yadda katafila ke rushe masallacin.

Asari Dokubo, ya kara da cewar Nyesom Wike, ya na ikirarin cewa babu masallaci, saboda haka karya ce, yake yi domin idan babu masallaci me ya kai ka wurin.

Ya ce wanda ya saye filin masallacin mutumin Okrika ne ‘Dan kabilar Ijaw mai suna  Dr. Sotonye Amadi.