Home Labaru Kano: Hukuncin Kotun Zabe Bai Shafi Dambazau Ba-APC

Kano: Hukuncin Kotun Zabe Bai Shafi Dambazau Ba-APC

238
0

Wani jigo a jam’iyyar APC, ya soki hukuncin da kotun zaben jihar Kano ta yanke, inda ta soke zaben dan majalisa  mai wakiltan mazabar Sumaila/Takai a majalisar wakalai, Shmasudeen Dambazau, kan hujjar cewa daga dan majalisar har jam’iyyarsa, babu mai shari’a a gaban kotun zaben.

Kranta Wannan: Kotu Ta Hana EFCC Kwace Kadarorin Yari

Kotun zaben ta umurci hukumar zabe ta INEC ta bayar da takardar shaidar cin zabe ga Surajo Kanawa, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben.

Da yake maida martani ga hukuncin kotun, jigon na APC wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce jami’iyyar PDP ta gabatar da shari’a ne akan Abdulrahman Suleiman Kawu Ismaila amma ba akan Dambazau ba, inda ya yi bayanin cewa tun farko wata babbar kotun tarayya ta yanke hukunci akan takarar Ismaila sannan ta umurci INEC da ta janye takardar shaidar cin zabensa sannan ta bayar da shi ga Dambazau.

Ya jadadda cewa ko kusa hukuncin bai da nasaba da Shamsudeen Dambazau, domin cewa babu inda aka ambaci sunansa a ko daya daga cikin takardun.