Home Labaru Taron Kasar Japan: Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Najeriya

Taron Kasar Japan: Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Najeriya

407
0
Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Najeriya
Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida daga taron da ya halarta a kasar Japan, wanda aka gudanar daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Agusta.

Karanta wannan: Cigaban Kasashen Afirka: Shugaba Buhari Zai Bar Najeriya Zuwa Kasar Japan

Daga  cikin hadiman shugaban kasa, mai suna Bashir Ahmaad, ne ya nuna bidiyon dawowar shugaban kasa, ta yanara gizo, inda ya ce  shugaba Buhari ya iso Najeriya ne ta babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, tare da ‘tawagar wadanda suka take masa baya zuwa garin Yokohama na kasar Jafan.

A wajen wannan taro da aka yi shugaban kasa Buhari ya gabatar da jawabi a madadin Najeriya a wani zama da aka yi, sannan kuma ya gana da wani Sarki a Birnin Tokyo, sannan ya yi amfani da wannan damar ya gana da manyan ‘yan kasuwan kasar waje domin ganin sun zo Najeriya sun buda kamfanoni.

Gwamnonin da aka yi tafiyar da su, sun hada da gwamnan jihar Borno  Babagana Zulum, da na jihar Kwara  Abdulrahman AbdulRazaq da kuma na Legas Babajide Sanwo-Olu tare da sauran manyan jami’an gwamnati.