Home Labaru Rundunar ‘Yan Sanda Ta Ce Bata Hana Likitoci Duba Wadanda Aka Harba...

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Ce Bata Hana Likitoci Duba Wadanda Aka Harba Ko Hatsarin Mota Ba

12
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ba ta taba cewa wani asibiti kada ya duba mutanen da suka samu harbin bindiga ko hadarin Mota har sai ya samo izini daga gare ta ba.

Sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya Alkali Baba, ya bayyana haka, yayin wani taron tattaunawa don gano hanyoyin aiki da dokar da ta tilasta duba wanda aka harba da bindiga a asibiti, wanda kungiyar lauyoyin Najeriya ta shirya.

Rundunar ‘yan sandan ta nuna rashin jin dadi a kan laifin da ta ce ana ɗora mata babu gaira babu dalili.

Babban Sufeton ‘yan sandan wanda mai magana da yawun rundunar Frank Mba ya wakilta ya ce, ‘yan sanda ba su taɓa hana likitoci duba mutumin da aka harba ko wanda ya yi hadari ko wanda aka cakawa wuƙa a asibiti ba, hasali ma suna aiki ne kafada-da-kafada da likitoci wajen kare rayukan al’umma.

Frank Mba ya kara da cewa, Likitocin Najeriya ba sa bukatar ko wane irin rubutu daga ‘yan sanda kafin su fara duba wadanda aka harba da bindiga ko wadanda suka yi hadarin Mota.

Alkali Baba ya tabbatar da cewa Asibitoci na da ‘yancin duba mutane da zarar an kai su asibitin,  abin da ake bukata shi ne lokacin da suke duba mutum suka ga harbin bindiga to su yi saurin sanar da jami’an ‘yan sanda.