Home Labaru Dakarun Sojin Najeriya Sun Dirar Wa ‘Yan Boko Haram A Jihar Borno

Dakarun Sojin Najeriya Sun Dirar Wa ‘Yan Boko Haram A Jihar Borno

131
0

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai na sojojin Najeriya sun yi wa mayaƙan Boko Haram ko ISWAP kwanton-ɓauna a Jihar Borno.

Wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a Alhamis din nan ta ce dakarun Bataliya ta 192 ne suka kai hare-haren ranar Laraba.

Janar Nwachukwu ya ce an kai harin ne da taimakon bayanan sirri bisa haɗin gwiwar dakarun ‘yan banga na Civilian Joint Task Force CJTF.

A cewar sa, an yi fafatawar a Rengye, wani wuri da aka yi amannar mahaɗar mayaƙan ce.

Kazalika, an kashe ‘yan bindiga huɗu yayin fafatawar sannan aka ƙwato bindiga kirar AK-47 biyu da jakar harsashi ɗaya da gurneti ɗaya da gwangwanin hayaƙi mai sa hawaye ɗaya.