Home Labaru Rikicin Manoma Da Makiyaya: Mutum Biyu Sun Mutua Jihar Taraba

Rikicin Manoma Da Makiyaya: Mutum Biyu Sun Mutua Jihar Taraba

13
0

Mutum biyu ne aka bada rahoton sun mutu yayin da wasu da dama suka  raunata sakamakon wata arangama tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Taraba.

Lamarin dai ya faru ne a yankin Gwomu na ƙaramar Hukumar Karim Lamido ranar Laraba.

Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Karim Lamido, Markus Hamidu, a tattaunawar sa da kafar talabijin na Channels ya ce  manoman sun fito ne sai suka ga garken shanu a bakin gonakin su, abin da ya haifar da tashin hankalin kenan.

Yace Sakamakon haka manoman suka kai wa makiyaya hari, inda suka kashe ɗaya daga cikin su, Su ma makiyayan suka kashe mutum ɗaya a harin ramuwar gayya.

A gefe guda kuma, wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Binnari na Karim Lamido, inda suka kashe mutanen da ba a san adadin su ba, tare da ƙona gidaje.

A cewar shugaban ƙaramar hukumar, an tura jami’an tsaro yankin da ke kan iyakar Jihar Filato.