Home Labaru Rufe Iyakoki: Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Ya Bayyana Matsayar Sa

Rufe Iyakoki: Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Ya Bayyana Matsayar Sa

294
0
Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda-IG Adamu
Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda-IG Adamu

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu, ya jaddada muhimmancin rufe iyakokin Nijeriya da kasashe makwaftanta domin cimma muradun ayyukan tsaro.

Muhammad Adamu ya bayyana wa manbema labarai haka ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya ce abin ya wuce batun fasa-kwaurin kayan abinci da lamurran kasuwanci, amma ya ce an yi hakan ne domin samun dakile shigo da makamai.

A baya dai Kakakin shugaban kasa Garba Shehu, ya taba yin bayani a kan yadda kasashen tafkin Chadi ke hada kai da Nijeriya domin murkushe ta’addancin da tuni ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da dukiya.