Home Labaru Tabargaza: Matashi Ya Zuba Guba Cikin Abincin ‘Yan Biki A Katsina

Tabargaza: Matashi Ya Zuba Guba Cikin Abincin ‘Yan Biki A Katsina

517
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Mudasiru Tanimu, bisa zargin zuba guba a cikin abin sha da aka raba wa mutane wajen wani biki a kauyen Barhim da ke yankin karamar hukumar Batagarawa.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ta SP Gambo Isah, rundunar ‘yan sandan ta ce, Tanimu ya hada kai ne  da wani matashi mai suna Nafi’u Umar domin zuba gubar a cikin abincin ‘yan biki.

Kakakin ya bayyana cewa, yanzu haka Nafiu ya cika rigar sa da iska bayan samun labarin an kama Tanimu.

 Ya ce matasan sun hada wata guba ne mai bugarwa suka zu ba a cikin Zoborodon da aka raba wa ‘yan biki, inda sakamakon haka hankalin wani mutum Iliya Musa da wata matashiya ya gushe nan take, bayan sun sha Zoborodon da matasan su ka zuba gubar a ciki.

Ya ce tuni an garzaya da su babban asibitin Katsina, inda likitoci su ka tabbatar cewa Musa ya mutu yayin da matashiyar kuma su ka ce ba ta cikin hayyacin ta.