Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce jam’iyyar APC za ta tabbatar ta bi dokar jam’iyya wajen zaben dantakarar shugaban kasa a shekara ta 2023.
Buhari ya bayyana haka ne, a wajen Taron Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar APC da ya gudana a Abuja.
Ya ce idan su ka bar APC ta ruguje bayan shekara ta 2023 ba su yi mata adalci ba, dole su bi abin da doka ta ce sannan a rika yi wa jam’iyya da’a, kuma ko kadan ba su ji dadin abin da ya faru a jihohin Imo da Bauchi da Zamfara ba.
Shugaba Buhari ya kara da cewa, dole sai an zabi shugabanni nagari tun daga zaben mazabu har zuwa matakin kasa sannan za a samu natsuwa da ci-gaba da kuma bin tsarin doka.
A karshe ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC su daina bin ra’ayin su ko nuna son kai da kin bin abin da tsarin dokar jam’iyya ya tanada.
You must log in to post a comment.