Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu, ya jaddada muhimmancin rufe iyakokin Nijeriya da kasashe makwaftanta domin cimma muradun ayyukan tsaro.
Muhammad Adamu ya bayyana wa manbema labarai haka ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya ce abin ya wuce batun fasa-kwaurin kayan abinci da lamurran kasuwanci, amma ya ce an yi hakan ne domin samun dakile shigo da makamai.
A
baya dai Kakakin shugaban kasa Garba Shehu, ya taba yin bayani a kan yadda
kasashen tafkin Chadi ke hada kai da Nijeriya domin murkushe ta’addancin da
tuni ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da dukiya.














































