Home Labaru Rikicin Shi’a: Kasar Iran Ta Nemi A Aike Mata Da Zakzaky

Rikicin Shi’a: Kasar Iran Ta Nemi A Aike Mata Da Zakzaky

639
0
Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Mabiya Akidar Shi’a Na Nijeriya
Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Mabiya Akidar Shi’a Na Nijeriya

Lauyan kotun Koli na kasar Iran, Muhammad Montazeri, ya nemi gwamnatin tarayya da kuma hukumar shari’a ta su ba jagoran mabiya akidar Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, damar zuwar kasar Iran domin a duba lafiyar sa.

Lauyan kotun Koli na kasar Iran, Muhammad Montazeri,

Kamfanin dillancin labarai na kasar iran mai suna Ahlul Bait, ya ce Montazeri ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya gabatar,inda ya ce  nemi hukumar shari’a wadda ta kasance uwa mabada mama wajen karbar koke da tabbatar da hakki, da ta bayar da belin Zakzaky jagoran kungiyar Shi’a a Najeriya.

Montazeri ya soki gwamnatin tarayya dangane da yadda take tafiyar da sha’anin ‘yan Shi’a a yayin da ya bayyana damuwa a kan yadda rashin lafiyar jagoran kungiyar ke ci gaba da ta’azzara.

Ibraheem Zakzaky, ya rasa idon sa daya na bangaren hagu a yayin da dakarun tsaro suka kai wani simame a gidan sa dake  Zaria fiye da shekaru uku da suka gabata, biyo bayan tare hanya mabiya akidar shi’a suka yi wa shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, a lokacin da zai wuce da tawagar sa a Zaria’.

Wannan lamari ya janyo salwantar rayukan mabiya shi’a da dama da suka hada da ‘ya’yan Zakzaky guda uku a sakamakon tarzomar da ta biyo baya.