Home Labaru Ci Rani: Sama Da Bakin Haure 100 Sun Bace A Teku

Ci Rani: Sama Da Bakin Haure 100 Sun Bace A Teku

1415
0

Hukumar Kula da Kaurar Baki ta Duniya ta ce, sama da baki 100 suka bace bayan kwale-kwalensu ya kife a tekun Kohms da ke kusa da gabar ruwan Libya.

Rahotannin sun ce, an yi nasara ceto mutane 145 daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su, yayinda ake zaton adadin wadanda suka bacen ya kai 150.

cikin wadanda hadarin ya rutsa da su

Charlie Yaxley da ke magana da yawun Hukumar Kula da Kaurar Baki ya yi karin bayani kan lamarin inda ya ce, “Akalla mutane 300 suka bar Khoms cikin kwale-kwalen katako kamar yadda muka samu labari, inda suka samu hadari a cikin teku, amma daya daga cikin kwale-kwalen ya dawo da mutane 150 da suka tsira daga hadarin, wannan adadi na da matukar yawa.

“Tabbas muna bukatar samun zaman lafiya a Libya ganin yadda bakin suka zama hanyar samun kudi, yadda suke biyan kudi domin samun hanyar wucewa zuwa Turai, sai a sanya su akan teku, yayinda kasashen Turai ke kauda ido akai, kuma sun hana a rika aikin ceto su, wannan ba hanya ce mai kyau ba.” in ji Yaxley.

Leave a Reply